An cire wa bankin UBA haramcin kudaden waje

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Najeriya na fama da karancin kudaden waje saboda faduwar farashin mai

Babban bankin Najeriya, CBN, ya cike bankin UBA daga cikin jerin bankunan da ya hana su hada-hadar kudaden waje, saboda bankin ya mika kudaden NNPC da ke hannunsa.

Wata sanarwar da CBN ta fitar ta ce dage haramcin a kan bankin na UBA zai fara aiki ne a ranar Alhamis.

Tun da fari dai CBN ta hana bankuna tara yin dukkan hada-hadar da ta shafi amfani da kudaden kasashen waje, har sai sun mika kudaden asusun kamfanin mai na kasar, NNPC da ke hannusu zuwa asusun bai daya na gwamnatin tarayya.

Masu sharhi a kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan matakin.

Tsohon mataimakin gwamnan CBN kuma mai sharhi a kan al'amuran tattalin arziki, Dokta Obadia Mailafiya ya bayyana wa BBC tasirin wannan matakin:

Labarai masu alaka