Kiristocin Nigeria sun soki ziyarar Kerry

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta ce ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya kawo, zata iya kara rura wutar tashe-tashen hankula masu nasaba da addini da kabilanci a kasar.

Hakan ya biyo bayan ganawar da Mista Kerry ya yi da shugabannin addinin musulunci da kuma wasu gwamnonin jihohin arewacin Najeriyar.

Kungiyar ta CAN ta kuma ce ziyarar ta sakataren harkon wajen na Amurka wata ajanda ce ta marawa yunkurin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na gallazawa kiristoci.

Bilkisu Babangida ta tattauna da Reverend Dokta Musa Asake, sakatare janar na kungiyar kiristocin ta Najeriyar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka