Za a kwashe mutane daga Daraya a Syria

Daraya a Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yadda hare-haren bama-bamai suka lalata gine-ginen birnin Daraya.

An cimma yarjejeniyar tsagaita-wuta, wadda za ta ba wa farar-hula da mayakan 'yan tawaye damar fita daga garin Daraya, wanda sojojin Syria suka dade da yi masa kawanya.

Gwamnatin Syria da wani kwamandan daya daga cikin manyan kungiyoyin 'yan tawayen da ke yankin sun ce a yau Juma'a ne za a fara kawshe jama'a daga garin, wadanda suka hada da farar-hula 4,000 da mayakan 'yan tawaye 1000.

Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa har yanzu ba a yi wani cikakken shirin da zai ba wa mayakan 'yan tawayen damar fita daga Daraya lafiya-lafiya ba.

Labarai masu alaka