Musulman Guinea sun kasa zuwa Hajji

Dubban Musulmai ne a kasar Guinea ke zaman jiran gawon shanu a birnin Conakry, saboda rashin takardar izinin zuwa aikin Hajji.

Fiye da maniyyata 7000 ne su ka yi rijistan zuwa aikin Hajji, shekaru biyu bayan haramcin da Saudiyya ta sanya wa kasar saboda barkewar cutar Ebola.

Kowanne maniyyaci ya biya kusan dala dubu biyar domin zuwa aikin hajjin.

Da dama daga cikin maniyyatan suna kwana ne a ginin cibiyar Musulmai ba tare da isasshen abubuwan amfanin yau da kullum ba.

Kadan ne daga cikin maniyyatan suka samu damar tafiya aikin hajjin a kasa mai tsarki.

Labarai masu alaka