Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Nigeria: Ana shagube da sunan Buhari

Image caption Halin rashin wadatar abin hannu na sanya 'yan Nigeria shiga wani yanayi na rashin walwala.

Wasu 'yan Nijeriya a baya-bayan nan, suna amfani da halin rayuwar da aka shiga a kasar, wajen yin shaguben siyasa ga shugabannin kasar, inda suke lakaba wa wasu nau'o'in abinci sunayen shugabannin.

Mutane na sanya sunan shugaban kasar, Buhari ko kuma Buhariyya da mataimakinsa Osinbajo wajen bayyana nau'o'in abinci ko yanayin tattalin arziki.

Wakilinmu na kano Mukhtari Adamu Bawa ya leka wani shagon mai sayar garin kwaki ko garin rogo a birnin, ga kuma rahon da ya aiko mana:

Labarai masu alaka