Nijar za ta fara jigilar alhazai

Muhammadou Issoufou Hakkin mallakar hoto
Image caption Jirgin Flynass mallakar Saudiyya ne dai zai yi aikin kwashe alhazan.

A Jamhuriyar Nijar, hukumar kula da tsare-tsaren aikin Hajji ta kasar ta ce a ranar lahadi ne za a fara jigilar maniyatan kasar zuwa Saudiyya.

Hukumar ta tabbatar da cewa tuni aka samu jirgi, kuma ana saran za a kammala jigilar alhazan kafin ranar 6 ga watan Satumba mai kamawa.

Mahukuntan Nijar sun ce kamfanin jirgin sama na Flynass mallakar kasau Saudiyya shi ne zai yi aikin jigilar alhazan.

A baya dai an shirya da kamfanin Air Nijar shi ne zai yi wannan aiki, amma daga bisani ya sanar da cewa ba zai iya ba saboda rashin jirage.

Lamarin da ya janyo tsaikon tafiyar maniyya ta aikin Hajjin bana a kasar.

Labarai masu alaka