An raba soyayyar shekara 62

Mista Gottschalk da maidakin sa Anita suna kukan rabuwa
Image caption Tun da ma'auratan sukai aure shekara 62 da suka wuce, ba su taba rabuwa ba.

Antilasta wa wasu ma'aurata tsofaffi 'yan kasar Canada da sukai aure shekara 62 da suka gabata zama a gidan tsofaffi daban-daban.

Tsoho Wolfram Gottschalk mai shekara 83 da mai dakinsa Anita mai shekara 81 na cike da jimami a hotunan da jikar su ta wallafa a shafukan sada zumunta da muhawara.

Ashley Baryik ta ce an tilastawa kakanin na ta rabuwa ne bayan gidan tsofaffin da aka kai su sun ce babu dakin da ma'auratan za su iya zama a ciki.

Mista Gottschalk da maidakinsa Anita ba su taba rabuwa ba duk tsahon lokacin da suka dauka su na tare, hotunan da jikarsu ta dauke su da kuma ta wallafa a shafukan sada zumunta da muhawara ya dauki hankalin mutane.

Ashley ta ce a rayuwarta ba ta taba daukar hoton da ya daga mata hankali kamar na kakannin ta su na share hawaye ba.

Tun dai a watan Junairun shekarar nan ne da aka shirya kai Mista Gottschald gidan tsofaffi, ita ma mai dakinsa Anita ta rubuta takardar ita ma ta na son bin mijin ta.

Labarai masu alaka