Pistorius: Kotu ta yi watsi da kara

Hakkin mallakar hoto epa

Wata mai shari'a a Afirka ta Kudu ta yi watsi da bukatar da masu gabatar da kara suka yi a kan hukuncin shekaru shida da aka yanke wa zakaran tseren nakasassun nan, Oscar Pistorius.

Mai shari'a, Thokozile Masipa ta ce babu wasu kwararan dalilai da za su sa bukatun su yi nasara.

A yanzu masu gabatar da karar suna da makonni uku domin su daukaka karar zuwa kotun koli na kasar.

Masu shigar da karar sun bayyana cewa hukuncin shekaru shida ya yi sassauci ga zakaran tseren wanda ya kashe budurwarsa, Reevasteenkamp.

Tun da fari dai an yanke wa Pistorius hukuncin shekaru biyar ne bayan kotu ta same da da laifin kisa ba da gangan ba.

Amma daga bisani aka yanke masa shekaru shida bayan samunsa da laifin aikata kisan budurwar tasa.

Mai shari'ar ta ce ba ta yanke masa shekaru 15 a kurkuku ba ne, saboda wasu dalilai masu kwari.

Da farko an ba wa Pistrous shekaru biyar a kurkuku domin kisan kai na kuskure, amma daga baya aka same shi da laifin kisan kai a kan roko.

Alkalin ya ce ta karkata daga shekara 15 da aka yanke mashi saboda dalilai masu tursasawa.

Labarai masu alaka