An kai hari gidan cin abinci a Somalia

Wani hari da aka kai a Somalia Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Al-Shabaab na yawan kai hari bakin teku a Somalia.

Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan cin abinci da ke gabar teku a Mogadishu, inda mutane bakwai suka rasu.

An dai fara kai harin ne da wata mota da aka dasa bam a cikinta, a wajen kulob din Banadir Beach da ke yankin Lido.

Sannan aka yi ta musayar wuta tsakanin 'yan bindigar da jami'an tsaro.

'Yan sanda sun ce an harbe biyu daga cikin maharan, yayin da aka cafke wani guda bayan an yi masa rauni.

Masu fafutuka na kungiyar Al-Shabaab sun sha kai hare-hare a birnin na Mogadishu da sauran sassan kasar Somalia.

Ko a farkon shekarar nan sun kai hari a irin wannan a yankin tekun Lido, inda mutane 19 suka hallaka.

Labarai masu alaka