An fara kwashe mutane daga Daraya a Syria

Fararen hula da yan tawaye sun fara barin garin Daraya da ke Syria bayan an cimma yarjejeniyar da ta kawo karshen kawanyar da gwamnati ta yi na shekara hudu.

Motocin daukar marasa lafiya da motocin Red Crescent sun raka mototcin farko da su ka bar garin da ke kusa da Damascus, babban birnin kasar.

'Yan tawayen za su je garin Idlib da ke karkashin ikon 'yan tawaye, yayin da fararen hula za su je gidajen da gwamanti ta samar.

A shekarar 2012 ne dai sojojin Syria suka yi wa garin Daraya kawanya, kuma a cikin watan Yuni ne kawai fararen hula suka samu sabbin kayan agaji.

Kafafen yada labarai na Syria sun ce za a fitar da maza masu dauke da makamai 700 da fararen hula 4,000 a wani bangare na yarjejeniyar.

Labarai masu alaka