Majalisa ta amince da gwamnatin Tunusia

Tunisia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daga kasar Tunisia guguwar sauyin da ta afkawa kasasahen larabawa ta fara kadawa.

Majalisar dokokin Tunisia ta kada kuri'ar amincewa da sabuwar gwamnatin kasar.

Firayim Minista, Youssef Shahid shi ne ke jagorantar sabuwar gwamnatin, wadda ta hadin-gwiwa ce, kuma ta samu kujera 167 daga cikin adadin kujeru 217 da ke majalisar.

Mista Youssef Shahid dai shi ne tsohon ministan harkokin cikin gidan Tunisia, kuma an nada masa mukamin Firayim Ministan ne bayan an kwance rawanin magabacinsa, wato Habib Essid, wanda aka kada masa kuri'ar yanke-kauna a watan jiya.