An kai hari hedikwatar 'yan sanda ta Turkiyya

Akalla 'yan sanda 11 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar fashewar wani abu a wajen hedikwatar 'yan sanda na Turkiyya.

Yayin da wasu 78 suka jakkata.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda bakin hayakin da ke fitowa daga ginin ya turnuke sama.

Kafafen yada labarai na Turkiyya sun ce an kai harin ne da wata mota mai dauke da bam, kuma sun daura alhakin harin a kan kungiyar masu dauke da makamai ta Kurdawa, PKK.

Kurdawa ne mafiya yawan mazauna garin Cizre, inda hedikwatar 'yan sandan ta ke, kuma garin na bakin iyakar kasar da Syria da kuma Iraqi.

A farkon shekarar nan ne dakarun Turkiyya suka gwabza fada da mayakan PKK a Cizre.

Labarai masu alaka