Amurka ta yi raddi ga kungiyar Kiristoci

Image caption Fadar White House

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, babban birnin Nageria ya maida raddi dangane da furucin da kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN, ta yi cewa ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya kai kasar za ta iya haddasa tashin hankali mai nasaba da addini ko kabilanci a kasar.

Ita dai Kungiyar CAN ta yi zargin cewa ziyarar Mr Kerry wata ajanda ce ta mara wa yunkurin gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari baya wajen gallazawa kiristoci.

Mukaddashin kakakin ofishin Jakadancin Amurka a Abuja, Mista Larry Socha ya ce zargin da kungiyar kiristoci suka yi ba shi da tushe ko kadan, yana jaddada cewa John Kerry ya kai ziyara Sokoto ne don tattauna da mabiya addinin musulunci da kirista a kan yanda za a dinga mutunta addinan juna, tare da shawo kan tsaurin ra'ayi a tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Mukaddashin Kakakin ya ce shafinsu na intanet na kunshe da cikakken bayanin da John Kerry ya yi a lokacin ziyarar tasa, don haka duk wani mai bukatar karin bayani yana iya ziyartar shafin.

A cewar Mista Larry Socha zaiyarar John Kerry ba ta da wata manufa face jaddada muhimmancin hadin kai, don haka idan da wta kungiya da ba ta fahinci lamarin ba, to ofishin jekadancin Amurka a shirye yake ya fayyace mata.

Labarai masu alaka