Amurka: Za a tantance jinin masu Zika

Gwajin jini Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption An dauki matakin gwajin jinin ne, dan hana yaduwar cutar a kasar da makofta.

Mahukunta a Amurka sun ce za a dinga gwajin dukkan jinin da ake ba da gudummuwarsa a kasar da sauran makwabta, don hana yaduwar cutar Zika.

A baya dai ba a gwajin Zika sai a jihar Florida da Puerto Rico, inda aka samu mutanen da suka harbu da cutar.

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka, ta ce gwajin jinin na taimakawa wajen gano jinin da aka ba da gudummuwarsa da ke kunshe da cutar Zika.

A bara ne dai cutar Zikar ta bulla a Brazil, kuma tun daga wancan lokacin ta ci gaba da yaduwa a yankin Amurka.