Al'ummar Gabon na zaben shugaban ƙasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan takara 10 ne ke fafatawa da shugaba mai ci yanzu Ali Bongo

A ƙasar Gabon, fiye da mutum dubu 600,000 suka fita rumfunan zabe yau Asabar don kada ƙuri'a a zaben shugaban ƙasar.

'Yan takara 10 ne dai ke fafatawa da shugaba mai ci yanzu Ali Bongo wanda ke neman wani wa'adin mulki na shekaru bakwai.

Shugaba Ali ya dare karagar mulki ne bayan rasuwar mahaifin sa shekaru bakwai da suka gabata inda ya bayyana kansa a matsayin wani dake ƙokarin kawo sauyi .

Abubawan da yake ta shela a lokacin yaƙin neman zabe sune irin ayyukan da gwamnatin sa ta samar a 'yan shekarun nan.

Sai dai masu sukar sa sun ce cin hanci ya dabaibaye harkar siyasar ƙasar, koda yake babban abokin hamayyar sa Jean Ping, wanda tsohon shugaban hukumar ƙungiyar tarayyar Afrika ne da su aka yi ta damawa lokacin zamanin mulkin marigayi Omar Bongo.

Akwai kuma wasu 'yan takarar ƙalilan kamar Bruno Ben Moubamba mai shekaru 49 da ya ce yana wakilitar 'yan siyasa ne sabbin jini.

Babban ƙalubalen da sauran 'yan takarar ke fuskanta shi ne rashin kudade.

A bisa tsarin zaben shugaban ƙasa a Gabon dai zagaye daya tak ake yi, wanda hakan ke nufin duk dan takara da ya fi samun yawan ƙuri'u a zaben shi ne zai kasance shugaban ƙasar.