Taron bunƙasa ƙasashen Afirka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Abe zai bayyana irin agajin da Japan za ta ba nahiyar Afirka

Firai Ministan Japan Shinzo Abe zai halarci wajen bude taron kwana biyu kan hanyoyin bunƙasa ƙasashen Afirka da aka bude yau a Kenya.

Wannan dai shine karon farko da ake yin irin taron a Afirka wanda ƙungiyar raya ƙasashen Afirka da ƙasar Japan din ke shiryawa.

Jami'ai sun ce Mista Abe zai yi amfani da wannan dama wajen bayyana irin agajin da Japan za ta bayar da sauran ayyukan da za ta yi wajen raya nahiyar Afirka.

Shekara da shekaru kenan da Japan ta ke taimaka wa wajen gudanar da ayyukan raya ƙasashen Afirka amma gudummuwar da China ke bayarwa ta sha gaban abubuwan da Japan din ke yi.

Labarai masu alaka