Nigeria: Kasuwancin mu ya ja baya sosai

Takardar Naira Hakkin mallakar hoto Nigeria State House
Image caption Tashin gwauron zabbin da dalar Amurka ta yi, ta taka rawa a koma bayan kasuwanci daga Nigeria zuwa kasashen waje.

A Najeriya mata sun dade suna harkar kasuwancin kasa da kasa, da su kan sari kayyaki musamman tufafi daga kasashen waje.

Wasu daga cikin irin wadannan mata kan bude shugana ne, yayin da wasu kan rika yawo ofisohi da ma'aikatu suna tallata kayan hajarsu

Sai dai da dama na kokawa da yadda kasuwancin ya samu koma-baya sakamakon faduwar darajar Naira a kasuwannin hada-hadar kudaden waje.

Aishatu Abdullahi ta dade tana zuwa kasuwanci Senegal da Switzerland, inda ta kan sari tufafin mata da na maza.

A hirarsu da Abdu Halilou ta nuna fargabar game da irin kalubalen da take fuskanta a kasuwanci:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti