Sojojin Najeriya na atisayen "Murmushin Kada"

Image caption Makasudin atisayen shine jaddada ƙwazon dakarun don fatattakar masu tada kayar baya

Rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da wani atisaye na musamman ga dakarunta data yiwa laƙabi da suna "murmushin kada".

Kakakin rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar Kanar Sani Usman Kukah Sheƙah ya shaidawa BBC cewa an ƙaddamar da atisayen ne a garin Sapele na jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriyar.

Ya ƙara da cewa makasudin atisayen wanda Babban Hafsan sojojin ƙasa na ƙasar Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya kaddamar shine jaddada ƙwazon dakarun rundunar wajen fatattakar masu tada kayar baya a yankin.

A kwanakin baya ne dai dakarun sojin Najeriya na musamman suka ƙaddamar da kai hare hare a sansanonin masu tada kayar baya dake fasa bututan mai a kasar.

Labarai masu alaka