Nigeria: Ana ci gaba da riga-kafin cutar Polio

Riga-kafin cutar Polio Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar ta sake bullowa bayan shafe tsahon lokaci ba bu mai dauke da ita a kasar.

A Nigeria, ana ci gaba da aikin riga-kafin cutar Shan Inna da aka soma a yankin arewa maso gabashin kasar a karshen mako.

Aikin dai ya biyo bayan gano wasu kananan yara biyu ne da cutar ta nakasa a jihar Borno da ke yankin na arewa maso gabas, kuma shi ne karon farko da aka samu wadanda suka kamu da cutar a Nijeriya cikin shekara biyu.

An dai shirya gudanar da rigakafin ne a matakai daban-daban sannu a hankali, har ya karade kasashen yankin Tafkin Chadi.

Matakin farko na yin riga-kafin za a faro ne daga jihar Borno, sannan jihohin Yobe da Adamawa.

Sai dai an nuna fargaba kan ta yadda za a shiga yankuna irin su Damasak, da Malamfatori, da Gwoza, da har yanzu ba su da cikakken tsaro a ciki.

Amma hukumomi a Nigeria na cewa, da taimakon sojojin da ke aikin fatattakar mayakan Boko Haram za a gudanar da aikin a duk inda ya kamata.

Labarai masu alaka