Wasu matafiya a Najeriya sun makale

Hakkin mallakar hoto

A Najeriya, daruruwan matafiya tsakanin jihohin Bauchi da Kano sun gamu da babbar matsala ta tsaiko sakamakon yankewar babbar hanyar da ta hade jihohin.

Hanyar dai ta datse ne sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da aka yi a jiya, kuma rahotanni na cewa wasu matafiyan, sun kwana ne a inda lamarin ya faru saboda sun makale.

Hanyar dai ta datse ne kusa garin Gadar-Maiwa dake karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Hukumomin gwamnati sun ce ana kokarin gyara hanyar ta yadda jama'a zasu iya ci gaba da bin ta.

Hanyar da ta datsen dai, ta hade jihohin Bauchi da Jigawa da kuma Kano ne, inda kuma aka yi ittifakin cewa dubban jama'a ne kan yi zirga-zirga a hanyar a kowace rana.

Labarai masu alaka