An kama Sinawa 'yan cuwa-cuwa a Spaniya

'Yan sandan Spaniya Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan cuwa-cuwar dai Sinawa 'yan uwansu suke taimako da takardun bogin.

'Yan sanda a Spaniya sun wargaza wani gungun 'yan cuwa-cuwa da ke ba da takardun bogi da ke ba wa Sinawa 'yan ci-rani damar yin aiki kamar sauran 'yan kasa.

'Yan sandan sun kama mutum 57 a Barcelona da Valencia, da San Sebastian da Las Palmas da ke tsibirin Canary.

Wakilin BBC ya ce a cewar 'yan sandan, Sinawan suna biyan madugan 'yan cuwa-cuwar, wadanda mata da miji ne dala dubu tara wajen yi musu takardun bogi da suka shafi aikin kwantaragi da na 'yan aikin gida, kuma da wadannan takardun ne ake samun izinin zama a kasar.

Labarai masu alaka