'Yan sanda mata a Turkiya zasu sa dankwali

Image caption Magoya bayan Erdowan sun yi nuni da yadda a ke barin 'yan sanda mata su sa dankwali a wasu kasashe

Turkiya ta dage haramcin sanya dankwali ga 'yan sanda mata a matsayin kayan su na aiki.

Daga ranar Asabar jami'an 'yan sanda mata suna da ikon sanya ƙaramin dankwali mai kama da hijiba amma sai su daura hula a sama matuƙar launi dankwalin daidai yake da kayan aikin 'yan sanda.

Jam'iyyar AK mai mulki dai ta dade tana matsin lamba akan a dage haramcin sanya dankwali ga 'yan sanda mata.

Masu sukar shugaba Recep Tayyip Erdogan sun zarge shi da neman kassara tsarin ƙasar Turkiya a matsayin wacce ba ruwanta da goyon bayan wani addini.

Sai dai magoya bayansa sun yi nuni da yadda a Scotland da Canada aka bar jami'an 'yan sanda mata su riƙa sanya dankwali.

Labarai masu alaka