Muna so Saudia ta janye jakadanta —Iraqi

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraqi ta bukaci kasar Saudi Arabia da ta janye jakadanta Mr Thamer-al-Sabhan a Bagadaza.

'Yan siyasa mabiya Shi'a sun sha nanata kiran da a janye Mr Sabhan, bayan wasu kalamai da ya yi kan shiga harkokin Iraqin da kasar Iran ke yi.

Kalamam na ikirarin cewa mayakan sa-kai da 'yan Shi'a ke marawa baya na kara haddasa rudani tsakaninsu da musulmai 'yan Sunni a kasar.

A makon jiya ne mahukuntan kasar Iraqi suka musanta wasu rahotannin kafafen yada labarai na yunkurin hallaka jakadan na Saudia.

Mr Sabhan ya maida martanin cewa, ko da ya bar kasar Iraqi ya rage na ma'aikatar harkokin wajen Saudia.

Ya kuma ce akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu.