Trump ya jaddada tsohuwar adawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dantakarar Republican Donald Trump

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya ce zai samar da na'urar da za ta taimaka wa mahukunta wajen sarrafa 'yan ci-rani.

Da yake jawabi a wajen yakin neman zabe a Iowa, Mista Trump ya ce na'urar za ta saukaka maida mutanen da bizarsu ta kare kasarsu ta asali.

Kazalika, ya jadadda goyon bayansa ga aniyar gina ganuwa a tsakanin Amurka da Mexico.

Haka kuma ya ce zai dakatar da tsarin ba da tallafi ga 'yan ci-rani.

Ya ce "za mu girka ganuwa a kan iyaka, kuma za mu fito da tsari a kasa baki daya da zai hana bakin-haure cin gajiyar tallafi."