Mutane 40 sun kamu da cutar Zika a Singapore

Hakkin mallakar hoto AP

Ma'aikatar lafiya a kasar Singapore ta tabbatar da karin mutane arba'in da suka kamu da kwayar cutar Zika wacce sauro ke yadawa a kasar.

Hukumomin sun ce duka wadanda suka kamu da cutar babu wanda ya yi wani bulaguro zuwa yankunan Latin Amurka da cutar ta Zika ke yaduwa.

Sun ce cutar ta yadu ne a cikin kasar ta Singapore.

Baki yan kasashen waje masu aikin gine-gine 36 ne aka gano dauke da kwayar cutar ta Zika, amma yanzu 34 daga cikin sun samu waraka.

Hukumar kare muhalli ta kasar Singapore ta dauki matakan hana sauro hayaiyafa, da suka hada da feshin maganin kwari a yankunan gidajen jama'a.

Labarai masu alaka