Kungiyar FARC ta dakatar da yaki a Colombia

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan tawayen kungiyar FARC a Colombia sun kawo karshen yakin da suke yi na sama da shekaru 50.

Hakan ta samu ne bayan shekaru 4 da soma tattaunawar tsagaita wuta a kasar Cuba.

Babbar kungiyar 'yan tawayen Colombiar ta FARC ta sanar da cewa ba za ta kara yakar gwamnatin kasar ba.

Jagoran 'yan tawayen FARC, Rodrigo Londono da ake kira Timochenko ya umurci mayakan kungiyar da su yi watsi da bindigogi, su rungumi zaman lafiya.

A nasa bangare, shugaban kasar Colombia, Juan Manuel Santos ya saka hannu a kan wata sanarwa da ke kira ga dakarun kasar da su dakatar da farautar mayakan 'yan tawayen na FARC.

Labarai masu alaka