EU: An yi magudi a zaben Gabon

Hakkin mallakar hoto Getty

Masu da sa ido kan zabe na kungiyar tarayyar Turai wadanda ke saka ido kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar a Gabon sun ce anyi magudi.

Shugaba wanda yake kan mulki, Ali Bongo da babban abokin hamayyar sa, Jean Ping, duk sun yi ikirarin samun nasara.

Mista Ping ya yi kira ga shugaban kasar ya amince da shan kaye da kuma kira ga mutanen Gabon su kare tsare kuri'unsu.

Amma tawagar Mista Bongo sun ce suna kan hanyar gudanar a manufarta na biyu.

A ranar Talata ne dai za a fitar da sakamako.

Tsohon shugaban kungiyar tarayyar Afirka, Mista Ping , yana kokarin hambarar da daular Bongo, wanda ya shugabancin kasar har tsawon shekara hamsin .