Ko kun san menene asalin "Sari"?

A duk lokacin da Lavanya Nalli ke yawo a cikin shagonta na sayar da tufafin Sari wanda matan India ke sakawa, fuskarta a cike ta ke da farin ciki.

Lavanya, 'yar shekara 32, ta yi bayani a kan irin alfaharin da ta ke yi da harkar kasuwancin da danginta suka shafe shekara 88 suna tafiyarwa.

Kakannin kakanninta ne dai suka bude shagon wanda ke kudancin birnin Chennai a shekarar 1928.

A shekaru da dama da suka gabata, kamfanin Nalli ya zama daya daga cikin kamfanonin da suka fi kwarewa wajen yi sari a Indiya.

Lavanya ta ce kamfanin Nalli ya yi suna kuma mutane na son tufofin sarin kamfanin saboda kyawunsu.

Kamfanin Nalli na samun kudin shiga sama da dala miliyan 100 a shagunasu 29 da ke Indiya da kuma wasu shagunan da ke kasar Singapore da jihar California da ke Amurka wanda haka yasa kasuwanci ke kara bunkasa.

Duk da cewa mata da dama a Indiya na amfani da tufafin kasashen yamma, Lavanya na amfani da horon da ta samu a harkar kasuwanci na shekaru da dama a wani kamfani wajen samar da sabon samfurin tufafin na Sari kuma ta kaddamar da kasuwancin intanet a kamfinin.

Sauya tsarin kwalliya

An san kamfanin Nalli da sakar sarin hannu, wanda masaka na yankin Kanchipuram da ke jihar Tamil Nadu a kudancin Indiya ke yi.

An san wadannan tufafin na sari da tsada da kyawun yadi da kaloli da kuma zane masu kyau.

An fi sanin su a matsayin kaya na musamman wadanda ake sakawa lokacin bukukuwan aure da sauransu kuma ana gadar da kyawawa daga cikinsu ga 'ya'ya da jikoki.

Su ma kuma suna da tsada, inda farashin wasu ke kaiwa dala 3,100.

Lavanya ta ce a lokacin da ta ke yarinya, babu yadda za a yi a ce ba ta nuna sha'awarta a kasuwancin ba, saboda mahaifinta da kakanta, a ko da yaushe suna tattaunawa a kan kamfanin a lokacin cin abincin dare.

A shekarar 2005 ne dai Lavanya ta fara aiki da kamfanin, a lokacin tana da shekara 21. Ta yi shekara 4 tana aiki sannan daga baya ta yanke shawarar ta karo ilimi a kan sababbin hanyoyin kasuwancin.

A lokacin da ta dawo Indiya a shekarar 2014, sai ta yi shekara guda da kamfanin sayar da tufafi na intanet da ake kira Myntra, sannan ta koma kamfanin danginta a shekarar 2015.

Bayan ta dawo ne danginta suka yanke shawarar cewa za ta iya jagorantar kamfanin na Nalli.

Tufafin kasashen yamma

Yayin da akasarin matan indiya ke saka sari a kasar, ba a daukar tsawon lokaci ba ka ga mata matasa sanye da tufafin kasashen yamma kamar su dogon wando na jins (Jeans) da riga shet (shirt) a titunan Indiya.

Suna sayen irin wadannan tufafi a shaguna irin su H&M da kuma Gap.

Goyon bayan ra'ayi

Nalli ba shi da niyyar fara sayar da tufafin kasashen yamma, amma Lavanya ta kaddamar da wasu sababbin nau'ukan tufafi na Kurtis da Salwar Kameez.

Kamfanin ya kuma samar da wasu nau'ukan Sari marasa tsada wadanda ake yi da yaduka masu araha. Hakan ya sa ana samun saukin farashin sari guda a kan $2.20, abin da bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da tufafin sari masu tsada.

Hakkin mallakar hoto

Lavanya ta ce ko da yake kasuwancin sari ne hanyar samun kudi ga kamfanin Nalli bai "sauya tufafin da ya ke samarwa zuwa irin wanda masu saye su ka fi so ba".

A yayin da Lavanya ta ke jagorantar ci-gaban kasuwanci a shafin intanet na kamfanin, domin sayar da kayan a kasashen duniya, tana da niyar ninka yawan shagunan zuwa shekakar 2020.

Ta ce danginta suna tallafa mata, musamman saboda tana kawo shawartarsu a kai a kai game da tsarin kasuwancin da ta ke kawowa.

Labarai masu alaka