Niger Delta Averngers ta tsagaita wuta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hare-haren Avengers dai sun taimaka wajen kassara tattalin arziki Nigeria

Kungiyar Niger Delta Avengers ta ce ta tsagaita wuta a hare-haren da ta ke kai wa kan bututayen mai da gas a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Litinin, kungiyar ta ce tana sa ran cewa gwamnati za ta nuna da gaske take wajen inganta yankin na Niger Delta.

Sanarwar wacce kungiyar ta wallafa a shafinta na internet ta yi amfani da kausasan kalamai wajen jan hankalin gwamnatin Nigeria cewa, ba za a kawo karshen matsalar hare-hare a yankin da karfin soja ba, don haka ta ce tattaunawa ita ce kawai mafita.

Ita ma dai kungiyar MEND mai fafutukar 'yantar da yankin Niger Delta ta shelanta cewa ita ma ta shiga tattaunawa da gwamnati, ta hannun kwamitin da Chief Edwin Clark ke jagoranta.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun ikirarin tsagaita wuta ba da wasu da ke da'awar yin magana da yawun kungiyar ta Niger Delta Avengers ke yi ba , to amma wasu daga baya suna nesanta kungiyar daga irin wannan mataki.