Amurka ta baiwa 'yan Syria 10,000 mafaka

Hakkin mallakar hoto Getty

Gwamnatin Obama ta ce, tuni ta cika alkawarin da ta yi na baiwa 'yan gudun hijirar Syria 10,000 mafaka domin su soma sabuwar rayuwa.

Cikin watan Satumbar bara shugaba Obama ya yi alkawarin bada mafaka ga 'yan Syria 10,000 da halin da suke ciki yafi tsananta.

Yanzu dai fadar White House ta ce, tana alfaharin cika wannan alkawari wata guda kafin wa'adin da aka ɗiba na yin hakan ya cika.

Gwamnatin Amurkan ta kuma ce, akalla 'yan gudun hijira 85,000 daga sassan duniya daban-daban ne zasu samu mafaka a Amurka cikin wannan shekarar.

Labarai masu alaka