Somalia na safarar dabbobi zuwa Saudia

Image caption Za a yi amfani da dabbobin ne domin aikin hajji

Ana safarar dabbobi masu dimbin yawa daga gabar ruwan Berbera da ke yankin Somali da ya ayyana 'yancin kansa zuwa kasar Saudi Arabia.

Tuni dabbobin da suka kai miliyan daya suka isa birnin Jiddah, sannan a makon gobe za a tura wasu dubu 500.

Gaba dayan dabbobin dai sai an yi musu gwaji dan tabbatar da cewa ba sa dauke da cuta, sannan a saka su a jirgin ruwa, domin kai su Saudiyar.

Nan da 'yan kwanaki kadan ne dai mabiya addinin musulunci za su fara aikin hajjin bana, wanda ya kunshi yanka dabbobi, da kuma yanka da ake yi domin babbar sallah.

Labarai masu alaka