IS ta kashe mutane da dama a Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin ya yi mummunan ta'adi

Likitoci a Yemen sun ce an kashe akalla mutane 60 a wani hari da aka kai wani rukunin gidajen 'yan tawaye da ke samun goyon bayan gwamnati a Kudancin birnin Aden.

Jami'ai sun ce wani dan kunar bakin wake ya tuka wata mota a cikin shahararriyar cibiyar 'yan bindiga, a lokacin wani taro kan daukar ma'aikata.

Kungiyar da ke da'awar kafa daular muslunci wato IS ta ce ita ta kai harin.

Tun bayan barkewar yakin basasa a watan Junairun 2015 ne dai ake rikici tsakanin 'yan tawayen Houthi mabiya mazhabar Shi'a da kuma dakarun gwamnati da kasashen duniya suka amince da ita.

Kawancen da Saudiya ke yi wa jagoranci dai yana kai hare-haren bama-bamai a kasar ta Yemen, don goyon bayan gwamnatin Abd-Rabbu Mansour Hadi.

Harin na bayan nan ya zo ne a daidai lokacin da ake yunkurin kawo karshen rikicin da aka shafe watanni 17 ana yi.

Akalla mutane 6,000 ne mafi yawansu fararan hula aka kashe, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Kimanin wasu miliyan biyu da rabi ne kuma aka raba da gidajensu.

Labarai masu alaka