Shin yaushe za a ceto 'yan matan Chibok?

Hakkin mallakar hoto Boko Haram
Image caption Hoton wata 'yar Chibok

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce a shirye gwamnatinsa take ta tattauna da 'yan Boko Haram domin ganin an saki 'yan matan Chibok fiye da 200 da 'yan kungiyar suka sace a 2014.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da 'yan jaridu a Kenya a karshen makon da ya gabata.

A baya-bayan nan ne dai kungiyar Boko Haram ta saki bidiyon da ke dauke da wasu daga cikin 'yan matan na Chibok.

A cikin bidiyon kuma wani mutum da ya rufe fuskarsa da kyalle ya nemi gwamnati ta saki 'yan kungiyar wadanda ke hannunta, kafin su saki 'yan matan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hoton 'yan Chibok da aka saki a watan Agusta

Sai dai Shugaba Buhari ya ce zai gana da 'yan kungiyar ne na asali ba na boge ba.

Ko a baya ma an sha samun yanayin da ake kokarin sasantawa tsakanin gwamnati da Boko Haram domin sakin 'yan matan amma yunkurin na cin karo da cikas.

Shin ko sau nawa ne aka samu irin wannan turka-turka a kan sharuddan sakin 'yan matan Chibok, tsakanin gwamnati da Boko Haram?

  • Buhari ya fada wa gidan talabijin na Aljazeera a watan Oktoban 2015 cewa zai tattauna da 'yan Boko Haram game da sakin 'yan matan Chibok.
  • A watan Disambar 2015, Shugaba Buhari, ta kafar talabijin, ya kara bayar da tabbacin tattaunawa da Boko Haram kan sakin 'yan matan na Chibok.
  • Shi ma tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ta bakin mataimakinsa na musamman, Hassan Tukur, ya sanar da shirin tattaunawa da Boko Haram kan sakin 'yan matan Chibok 219.
  • A watan Mayun 2014 ne kuma gwamnatin ta Goodluck Jonathan ta nemi dan jaridar nan Ahmed Salkida da ya jagoranci shirin sasantawa da nufin sakin 'yan matan na Chibok.
  • Har wa yau dai, a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, wani dan kasar Australia, Stephen Davis, ya shiga tsakanin gwamnati da Boko Haram da manufar sakin 'yan matan Chibok, a watan Aprilun 2015 amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Masu sharhi dai na ganin cewa akwai matsaloli a dukkannin bangarorin biyu wadanda suka kai ga kasa cimma yarjejeniya.

Yayin da wasu ke suka cewa gwamnati ba da gaske take yi ba, wasu na da ra'ayin cewa har yanzu ba a samu 'yan kungiyar Boko Haram na ainahi ba, al'amarin da ya sanya yarjejeniyar kan ci tura.

Ko za a kai ga tattaunawar domin sakin 'yan matan na Chibok? Lokaci ne kawai zai iya tabbatar da hakan.

Labarai masu alaka