Apple zai biya harajin Euro Billion 13 ga EU

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanin Apple yana da masu hulda da yawa a duniya.

Tarayyar Turai ta yanke cewa kamfanin Apple zai biya Euro biliyan 13 na harajin da kamfanin ya rage bai biya ba a Jamhuriyar Ireland.

Hakan dai ya biyo bayan wani bincike da ya gano badakalar shekara uku ta rage biyan harajin da kamfanin ya yi.

Jaridar Financial Times ta rawaito cewa idan har an amince da biyan harajin wanda zai zama biliyoyin Euro, to zai zama hukuncin da ya fi kowanne tsanani a nahiyar Turai.

Sai dai kuma ana ganin kamfanin na Apple da gwamnatin Ireland duka za su daukaka kara kan al'amarin.

Bisa ga dokar Tarayyar Turai, Hukumomi Masu Karbar Haraji na cikin kasa ba su da hurumin yafe wa wani kamfani haraji.

Jami'an Tarayyar Turai sun ce a 1991 da 2007 gwamnatin Ireland ta yi wasu dokoki da suka ba wa kamfanin na Apple damar rage yawan harajin da ya kamata ya biya.

Labarai masu alaka