Gabon: Ana jiran sakamakon zaɓe

Jami'an tsaro a Gabon suna sintiri a titunan babban birnin kasar Libraville, yayin ake ci gaba da jiran sakamakon zaɓen shugaban kasar da aka gudanar a karshen mako.

Shugaba mai ci, Ali Bongo da kuma babban abokin adawarsa, Jean Ping dukka sun yi ikirarin samun nasara a zaben.

Tuni dai sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon ya yi mgana da dukkansu biyu ta waya domin kwantar da hankulla.

Ban Ki Moon ya buƙaci 'yan siyasar biyu su yi kira ga magoya bayansu su kwantar da hankali yayin da ake jiran sakamakon zaben.

Ali Bongo, da mahaifinsa marigayi Omar Bango sun kwashe kusan rabin ƙarni suna mulkin ƙasar ta Gabon.

Labarai masu alaka