Italia: An ceto bakin haure 6500

Masu tsaron gabar tekun Italia sun ce, sun ceto bakin haure dubu 6 da dari 5 a tekun Bahr Rum ranar Litanin.

Hukumar kula da tsaron gabar tekun ta ceto mutanan ne lokacin da take gudanar da wani aikin hadin gwiwa da bataliya 40.

Cikin shekaru da dama, wannan Litanindin ta zama mafi kasancewa mai cike da dumbin aiki da ma'aikatan suka taba fuskanta a aikinsu na ceton rayukan bakin haure a teku.

Wasu ma'akatan sun yi kokarin ceto bakin haure 'yan kasar Eritriya da Somalia lokacin da suke tsunduma cikin ruwan teku da zummar gaggauta cimma jirgin ruwan ma'aikatan ceton.

Dubban 'yan Afirka, daga cikin su da dama na neman zuwa turai ne, don samun arziki, abun da ya sa suke shiga Ζ™ananan jiragen ruwa wadanda basu da inganci daga gabar ruwan Libya.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun fito ne daga yankunan da ake yaki a gabas ta tsakiya da Afghanistan.

Labarai masu alaka