Saudiyya ta sallami na'iban limamai 10,000

Ma'aikatar harkokin addinin musulunci ta Saudiyya ta sallami na'iban limamai 10,000 domin tsuke bakin aljihu.

Wannan mataki zai sa a yi tsimin Riyal miliyan 360.

Jaridar Saudi Gazette ta ce, an kuma baiwa na'iban limaman zaɓin, ko su zama cikakkun limamai su riƙa gabatar da salloli biyar, ko kuma su nemi wata sana'ar.

Wasu dai na sukar na'ibai a Saudiyya, inda suke cewa, akasari basa yin aikin komai, kuma suna karɓar albashin Riyal 3000 kowanne wata.

Sai dai kuma wasu a kasar sun koka cewa, sallamar na'iban daga aiki zata haifar da ƙarancin limamai da za su rika jagorantar salloli biyar.

Masu wannan ƙorafi sun ce, za a samu matsala a duk lokacin da limamai suke hutunsu na shekara-shekara.

Labarai masu alaka