A yi taron PDP a Abuja –– Jibrin

Kwamitin amintattu na Jam'iyyar PDP a Nigeriyya ya bukaci kwamitin gudanarwa na jam'iyyar da ta dauki mataki na fara shirya babban taron jam'iyyar nan gaba kadan a Abuja don zaben shugabannin Jam'iyyar.

Mambobin kwamitin amintattun sun ce sun dauki wannan mataki a ci gaba da yunkurin da suke yi na kawo karshen takaddamar shugabanci da ya dabaibaiye jam'iyyar.

Yanzu bangaren Sanata Ali Madu Sheriff da kuma bangaren Sanata Ahmed Makarfi ne dukkanin su ke ikirarin shugabancin Jam'iyyar PDP.

Senata Walid Jibrin, shugaban kwamitin amintattun, ya shedawa BBC cewa lokaci ya yi da ya kamata su sa baki dan kawo karshen rigingimun da jam'iyyar ta ke fama da su.

Labarai masu alaka