Shugaban Facebook ya iso Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mark Zuckerberg ya zo Najeriya, a wata ziyarar karon farko a Afirka.

Shugaban shafin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg ya sauka a birnin Legas, na Najeriya, a ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka.

Mista Zuckerberg ya gana da matasan da suke harkar kamfanonin fasahar zamani domin ya kara musu karfin gwiwa.

Wata sanarwa da kamfanin Facebook ya fitar ta ce Mista Zuckerberg ya je Najeriya ne domin harkokin bincike na kasuwanci.

"Mark zai yi saurari jama'a, ya dauki darasi da kuma hikomomi kan yadda Facebook zai taimaka wurin bunkasa harkokin sadarwa a Afirka," in ji sanarwar.

Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa "zan dauki darasi kan yadda ake kafa kananan kamfanoni a fannin sadarwa a Najeriya.

"Wannan wuri ya bani sha'awa sosai, kuma a shirye nake na koyi abubuwa masu da dama".

Kididdiga ta nuna cewa mutanen Najeriya sun fi na kowacce kasa masu ma'amala da kafar sada zumunta ta Facebook a nahiyar ta Afirka.

Ya taso ne daga kasar Italiya, inda ya gana da Paparoma Francis, sannan ya yi magana kan muhimmancin samarwa mutane damar yin hulda juna da yanar gizo musamman a wuraren da babu manhajar.

Labarai masu alaka