An tsige shugabar Brazil Dilma Rousseff

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An zarge Dilma da yin ba dai-dai ba a kasafin kudi

Majalisar dokokin Brazil ta kada kuri'ar tsige Shugaba Dilma Rousseff sakamakon aikata almundahana a kasafin kudin kasar da ake zargin ta yi.

Matakin ya kawo karshen shekara 13 da jam'iyyarta ta Workers Party ta yi a kan mulki.

Uwar gida Rousseff ta musanta zargin da aka yi mata.

Sanatoci 61 ne suka kada kuri'ar tsige ta, 20 kuma suka goyi bayanta, abin da ya sa aka samu kaso biyu cikin uku da ake bukata gabanin tsige ta.

Mukaddashin shugaban kasa Michel Temer zai cika wa'adin mulkinta wanda zai kare ranar 1 ga watan Junairun 2019.

A cikin watan Mayu ne aka dakatar da Rousseff bayan majalisar dattawan kasar ta kada kuri'ar ci-gaba da yunkurin tsige ta.

An dai zarge ta da sauyawa kudade muhalli a cikin kasafin kudin gwamnati, wanda ya saba da dokokin Brazil.

Sai dai tubabbiyar shugabar ta bayyana tsige ta da cewa juyin mulki ne.

Ta ce da ma tun da aka sake zabar ta abokan hamayya na cikin gida a jam'iyyarta suke yunkurin ganin bayanta.

Ta kara da cewa an tsige ta ne kawai saboda ta bayar da dama a gudanar da bincike mai zurfi a kan zarge-zargen cin hanci, abin da ya kai ga tuhumar wasu gaggan 'yan siyasa.