An gano hodar-Iblis a kamfanin Coca-Cola

Hakkin mallakar hoto Getty

An gano hodar-Iblis wadda kudinta ya kai Fam miliyan 42, a wani kamfani da ake yin lemon Coco-Cola, a Fransa.

An dai kai akwatinan lemo kamfanin na Coca-Cola tare da hodar-Iblis wadda aka boye a cikin wasu jakunkuna, daga Kudancin Amurka.

Yanzu haka, ana gudanar da bincike dangane da al'amarin, a kauyen Signes da ke kudancin Faransa.

An wanke ma'aikatan Coca -Cola daga hannu a al'amarin, kuma masu bincike na ƙoƙarin gano daga wurin da aka kawo hodar ta Iblis.

Labarai masu alaka