Donald Trump zai ziyarci Mexico

Hakkin mallakar hoto
Image caption Donald Trump a gaban magoya baya

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump zai ziyarci kasar Mexico, ranar Laraba.

Wannan dai yana zuwa ne 'yan sa'o'i kafin dan takarar ya fitar da wasu matakan da yake ganin zai dauka, idan ya ci zabe, kan 'yan cirani, a wani jawabi da ya gabatar.

Mista Trump ya wallafa a shafinsa na twitter cewa yana son yin ido-biyu da shugaban Mexico,Enrique Pena Nieto wanda ya gayyace shi da Hillary Clinton.

Shi dai Donald Trump ya soki 'yan cirani 'yan kasar Mexico da ke Amurka, a lokacin yakin neman zabensa, a inda ya sha alwashin gina katanga tsakanin kasashen biyu.