Yawan giwayen Afirka sun ragu

Hakkin mallakar hoto

Yawan giwayen Afirka ya ragu da kaso daya cikin uku a shekaru goma da suka wuce.

A wani bincike na farko na nahiyar da aka yi daga jirgin sama, ya nuna cewa an kashe kalla giwaye dubu 144.

Kididigar giwaye, wacce aka gudunar ta kunshi fadin murabba'in kilomita dubu dari biyar a yankin hamada a kasashse 18, wanda aka yiwa take da 'kididdigar giwaye mafi girma'.

Shekaru biyu aka shafe ana gudanar da binciken, wanda Paul Allen shugaban Microsoft ya dauki nauyi.

Farautar giwaye da ake yi yanzu ba a bisa ka'ida ba, zata iya sa ragowar giwaye 430,000 da suka rage a Afirka su bata a shekaru goma masu zuwa.

Sama da kashi 40 cikin dari na giwayen Nahiyar na kasar Botswana, amma yanzu, masu farautarsu ba bisa ka'ida ba sun kafa musu kahon zuka.

Labarai masu alaka