An kashe wani kwamandan IS

Kungiyar IS ta sanar da mutuwar Abu Muhammad Al-Adnani wanda ya kasance daya daga cikin manyan kwamandojinta.

Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon daga nata bangare, ta sanar da cewa marigayin shi ne babban mai kula da ayyukan kai hare haren da aka shirya kuma ake kaiwa a waje, na kungiyar, bayan kasancewar shi kakakinta.

A yanzu haka dai Amurka na gudanar da kididdiga da kuma bincike kan hare-haren da ta kai ta sama a shiyyar Aleppon kasar Syria a ranar Talata.

Wani shafin sadarwa na internat mai alaka da kungiyar ta IS ya bayar da cikakken bayani game da yadda Abu Muhammad Al adnani ya mutu.

A Shekaru biyu da suka gabata, marigayi, Abu Muhammad Al Adnani ya umarci magoya bayan kungiyar ta IS da su yi ta kai hare-hare a kasashen yammacin duniya duk inda suke iya kaiwa, bakin rai bakin fama, har sai sun ga abin da ya hana tulu gashi.

Labarai masu alaka