Najeriya:Mawuyacin halin tattalin arziki

Tattalin arzikin giwar Afirka watau Nijeriya, ya shiga wani mawuyacin hali.

A karon farko cikin shekaru goma, kasar na fuskantar koma-bayan tattalin arziki.

Wasu alkaluma na sulusi na biyu na wannan shekara, wadanda ake sa ran fitarwa nan gaba a hukumance, na nuni da cewa bunkasa ta ragu matuka, a tattalin arzikin kasar.

Tattalin arzikin Nijeriya dai shi ne na biyu mafi girma a nahiyar Afirka, watau bayan da a cikin 'yan kwanakin nan, Afirka ta Kudu ta sha gaban Nijeriyar ta zama ta daya a girman tattalin arziki.

Wasu 'yan Nijeriyar da dama na cewa ba su taba shiga yanayi mai tsauri irin na wannan lokaci ba.

Labarai masu alaka