'Tattalin arzikin Nigeria zai farfaɗo'

Image caption Rashin aiki ya kazanza a 'yan kwanakin nan

Gwamnatin Nigeria ta ce, akwai fatan cewa, tattalin arzikin kasar zai farfado nan da karshen shekara.

Kakakin shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya ce, ana daukar matakai dake nuna alamar tattalin arzikin zai soma farfadowa.

Ya kuma ce, abubuwan da suka haddasa karayar tattalin arzikin Nigeria sun hada da fasa bututan mai a yankin Niger-Delta.

Malam Garba Shehu ya kuma ce, faduwar farashin mai ita ma ta kara jefa tattalin arzikin Nigeria cikin halin da ake ciki yanzu.

Gwamnatin Najeriyar ta ce, ta zo ta karbi mulki ne bayan gagarumar barna da ta tallafa wajen karya tattalin arzikin kasar.

Wasu alkaluma da Hukumar Kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta fitar sun nuna cewa kasar ta samu koma-baya a tattalin arzikinta.

Alkaluman da hukumar ta saki sun nuna an samu tawayar kaso biyu cikin dari na arzikin kasar da mutanenta, a watanni ukun da suka gabata.

Hakan dai na nuni da cewa, Najeriya ta fada cikin kangin tattalin arzikin da ya fi kowanne a tsawon shekara goma.

Da man ko a watanni ukun farko na bana, tattalin arzikin ya samu komada da kaso 1.70 ne kawai.

Sai dai kuma alkaluman sun nuna cewa komadar ta wannan lokacin ba ta kai ta watanni ukun farko na mulkin shugaba Buhari ba, a 2015.

Hukumar ta Kididdiga dai ta ce kasar ta samu tawayar arziki da kaso 2.35.

Waikilin BBC a Legas Martin Patience ya ce wannan dai bai zo wa 'yan kasar da mamaki ba bisa la'akari da irin mawuyacin halin da jama'a ke ciki ta fuskar tattalin arziki.

Karya darajar Naira

Najeriya dai tana fama da koma-baya sakamakon tabarbarewar farashin mai a kasuwar duniya.

Al'amarin dai ya sanya kasar fuskantar nakasu a kudaden shigarta baya ga faduwar darajar kudin kasar da kuma tashin gwauron zabbin da farashin kayayyaki ya yi.

Hauhawar farashi a Najeriya

Daga shekarar 2015 zuwa 2016

2015

Shinkafa —N10,000

2016

Shinkafa —N18,000

  • 2015 Masara — N3,500

  • 2016 Masara — N17,000

  • 2015 Siminti — N1,500

  • 2016 Siminti — N2,300

Getty

Kasar dai wadda ke jerin kasashen da ke kan gaba wajen albarkatun man fetur a nahiyar Afirka, ta dogara ne kacokan bisa kudaden da ake samu daga sayar da man.

Kuma wasu na ganin faduwar farashin man ne a kasuwar duniya ya haddasa wa kasar halin da take ciki.

Sai dai kuma wasu masu fashin baki na ganin cewa irin tsare-tsaren da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka ne suka kara janyo tabarbarewar al'amuran.

Masana na cewa babban dalilin da ya kara ta'azzara koma-bayan da tattalin arzikin kasar ya samu shi ne dagewar da gwamnatin ta yi kan cewa ba za ta rage darajar kudin kasar ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rashin ciniki na addabar 'yan kasuwa da dama saboda faduwar darajar Naira

To amma daga bisani, shugaba Buhari ya mika wuya kan batun rage darajar ta Naira, a inda aka kyale farashin Nairar a bude a kasuwa.

Hakan kuwa masana sun ce shi ne dalilin da ya kawo tashin gwauron zabbin farashin kayan masarufi da dai sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

Gwamnatin dai ta ce tana son bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma ribato masu son sanya hannun jari daga kasashen waje.

Ta kuma fito da tsare-tsare da za su tabbatar da rage shigo da kaya cikin kasar.

Labarai masu alaka