Gabon: An kame fiye da mutane 1,000

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban jam'iyyar adawa ta Gabon, Jean Ping

Gwamnatin Gabon ta ce ta kama mutane fiye da 1,000 yayinda jami'an tsaro ke kokarin maido da doka da oda bayan bayyana sakamakon zaben da ake takaddama a kai.

Shugaba Ali Bongo ya yi tir da magoya bayan 'yan adawar da suka hau tituna a ranar Laraba inda suka kone ginin Majalisar dokoki wuta.

Tun da farko mutumin da shugaban Gabon Ali Bongo ya kayar a zaben ranar Asabar, Jean Ping, ya ce jami'an tsaro sun shiga hedikwatar jam'iyyarsu, a inda suka kashe mutum biyu sakamakon bude wuta.

Jami'an tsaro na kasar dai sun kai wani samame hedikwatar jam'iyyar, bayan zargin wasu bata-gari da cinna wa majalisar dokokin kasar wuta.

Magoya bayan Ping dai suna ta faman zanga-zanga tun bayan fitar da sakamakon zaben da aka yi wanda ya nuna shugaba Ali Bongo ne ya lashe zaben.

Masu zanga-zangar dai suna zargin gwamnati ne da yin magudi.

Sakamakon zaben dai wanda aka sanar ranar Laraba, ya bayyana shugaba Bongo da wanda ya yi nasarar lashe zaben da kaso 49.8, a inda shi kuma Jean Ping ya samu kaso 48.2.

Labarai masu alaka