Gabon: An ƙona majalisar dokoki

Masu adawa da shugaban Gabon, Ali Bongo sun ƙona majalisar dokokin kasar.

'Yan adawar sun fusata ne bayan an bayyana cewa, shugaban mai ci ne ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar.

Mazauna birnin Libreville sun ce, ta ko'ina ana iya hango hayaƙi ya tirniƙe yayin da dare ya soma shigowa.

Kafin a kai ga wannan sai da 'yan sanda suka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa magoya bayan Jean Ping.

Sakamakon zaben dai ya nuna shugaba Bongo ya yi nasara da ƙasa da ƙuri'u dubu shida.

A yankin da shugaba Bongo ya fito sakamakon zaben ya nuna cewa, kusan kowa ya fito jefa kuri'a.

Iyalan gidan Bongo dai sun kwashe kusan rabin ƙarni suna mulkin kasar ta Gabon.

Labarai masu alaka