Gabon: An kama 'yan adawa 1000

Hakkin mallakar hoto

Gwamnatin Gabon ta kama mutane fiye da dubu a rana ta biyu a ci gaba da zanga-zangar da 'yan adawa suke yi domin nuna rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar.

Rahotanni sun ce, an kashe mutane uku a Libreville babban birnin kasar.

'Yan adawa sun ce, an yi maguɗi a zaben da shugaba mai ci Ali Bongo ya lashe da takazarar kuri'u kadan.

Dan takara na 'yan adawa Jean Ping, wanda yanzu ya buya, ya yi kira ga shugaba Bongo ya sauƙa daga muƙaminsa.

Amma ministan harkokin cikin gida na kasar ya ce, shugaban kasar ya lashe zaben bisa gaskiya da adalci.

Tuni majalisar dinkin duniya, da Amurka, da Faransa suka yi kiran a kwantar da hankulla.

Labarai masu alaka