Michel Temer ne sabon Shugaban Brazil

Hakkin mallakar hoto AP

An nada Michel Temer a matsayin sabon shugaban kasar Brazil kuma zai karashe wa'adin Ms Rousseff har sai 1 ga watan Janairun shekarar 2019.

A baya dai, dan siyasar na jam'yyar masu matsakaicin ra'ayin mazan jiya na PMDB, ya yi rikon kwarya na shugabancin kasar lokacin da ake kokarin tsige Dilma Rousseff.

A lokacin da yayi ganarwar farko da ministocinsa bayan an tsige Dilma, Mista Temer ya ce nada shi a matsayin shugaban kasa na nufin "sabon zamani"

A ranar Laraba ne dai 'yan majalisar dattawan kasar Brazil suka kada kuri'ar da ta tsige shugaba Dilma Rousseff daga kan kujerarta saboda zarginta da sama da fadi da kasafin kudin kasar.

Sai dai Ms Rouseff ta musanta zargin da ake mata.

Hakan dai ya kawo karshen shekaru 13 da Dilma ta shafe tana mulki a karkashin jam'iyyar masu tsatsaurar ra'ayi.

Labarai masu alaka